An kashe 'yan leken asirin Amurka

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Irin wadannan hare-hare daga kungiyar ta al-Shabaab dai ba wani bakon abu ba ne a Somaliya.

Kungiyar Al-Shabaab ta Somalia ta ce ta kashe mutane hudu da take zargi 'yan leken asirin Amurka ne.

Amurka dai na goyon bayan gwamnatocin Habasha da Somalia.

An kashe mutanen ne a garin Bardhere a ranar Talata bayan wani alkalin kungiyar ta Al-Shabbab ya same su da laifin goyon bayan hukumar leken asirin Amurka, CIA da sauran kungiyoyin da ke fada da kungiyar.

A makon da jiya ne dai jami'an gwamnatin Somalia suka ce an kashe wani babban jami'in kungiyar, Abdishakur Tahlil, lokacin da aka kai masa hari ta sama.