Bam ya hallaka mutane 30 a Yemen

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan Alka'ida sun hallaka dubban mutane a Yemen

Wata mota makare da bam ta fashe a kwalejin horasda 'yan sanda a Sanaa babban birnin Yemen inda mutane kusan 30 suka rasu.

Jami'an tsaro sun ce wasu mutane fiye da 50 sun rasu sakamakon harin.

Motar ta fashe ne a lokacin da mutane suka taru a gaban ofishin 'yan sanda domin daukarsu aiki.

Wannan shi ne hari na baya-bayanan da aka kai a makonnin nan a Yemen.

Ana zargin kungiyar Alka'ida a kasar da kai wannan harin.