'Yan Boko Haram sun kone garin Baga

Garin Baga na jihar Borno Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Garin Baga na jihar Borno

Jama'ai a karamar hukumar Kukawa da ke jihar Bornon Najeriya sun ce 'yan Boko Haram sun kone garin Baga kurmus.

Shugabana karamar hukumar, Musa Alhaji Bukar Kukuwa, ya shaidawa BBC cewa 'yan Boko Haram din sun kai hari a garin ne ranar Laraba, inda suka yi ta harbe-harbe na kan-mai-uwa-da-wabi.

Ya bayyana cewa an kashe mutane da dama, sannan kowa ya fice daga garin.

A cewearsa babu yadda za a yi su shiga garin, ballantana su dauko gawarwakin mutanen da 'yan Boko Haram din suka kashe.

Karin bayani