Boko Haram: 'Yan gudun hijira 3000 sun shiga Chadi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan gudun hijirar sun tsere saboda tsoron Boko Haram

Hukumomi a Chadi sun ce 'yan gudun hijira daga Najeriya fiye da 3,000 ne suka shiga kasar saboda tsoron hare-haren 'yan Boko Haram.

Firai Ministan kasar, Kalzeube Pahimi Deubet ya shaidawa jakadu a birnin N'Djamena cewa 'yan gudun hijirar sun yi ta kwarara cikin kasar tun daga tsakiyar watan Disamba.

Ya kara da cewa, "ya zuwa yanzu mun tantance 'yan gudun hijira 3,000 da suka zo daga Najeriya, sannan akwai 'yan kasarmu 543 da suka dawo gida daga Najeriyar saboda tsoron hare-haren 'yan Boko Haram".

Firai Ministan ya ce suna fargabar cewa hakan zai kai ga faruwar babban bala'i, yana mai yin kira ga kasashen duniya su kai wa 'yan gudun hijirar agaji.