'Yansanda na neman maharan Charlie Hebdo

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan sanda na neman Cherif da Said Kouchi

Ana gudanar da wani gagarumin sintirin yansanda a arewa maso gabacin Paris, a inda mutane 2 da aka yi amannar ganin 'yan gwagwarmayar Islaman nan da suka kai hari a mujallar barkwancin nan ta Charlie Hebdo.

'Yansanda dauke da makamai sun yiwa kauyen Longpont,dirar mikiya, a inda shedu suka ce jami'ai na gudanar da binciken gida -gida.

An dai saka yankin na Picardy cikin shirin ko ta kwana.

A wani lamarin kuma an kashe wata yarsanda a lokacin da wani mutum ya bude wuta a wani wurin da aka yi hadarin mota a wata Unguwar bayan birnin Paris.

Wani dan bindiga ya kashe wata 'yar sanda a Paris, kwana guda bayan masu tsatsauran ra'ayin Musuluncin sun kashe mutane 12 a ofishin wata mujallar barkwanci.

Wani mutum kuma ya ji mummunan rauni a lokacin harin da ya auku a garin Montrouge da ke kudancin kasar, kafin dan bindigar ya arce.

Babu tabbas ko wannan lamarin na da alaka da kisan da aka yi a mujallar Charlie Hebdo, abinda ya jefa Faransawa cikin zullumi.

'Yan sanda sun damke mutane bakwai a cikin dare a yayinda suke neman mutane biyu da ake zargi da kisan ruwa ajallo.

An ba da sammacin kama Cherif da Said Kouachi wadanda aka ce suna da "hadari dauke da makamai", sannan mutum na uku da ake zargi ya mika kansa.

To dangane da harin na kamfanin Mujallar Charlie Hebdo, kasar ta Faransa ta ce a ranar Alhamis za a yi jimamin wadanda suka mutu a harin.