Jonathan zai kaddamar da kamfe a Lagos

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jonathan ya ce ya yi ayyuakan ci gaban Najeriya, sai dai wasu 'yan kasar sun ce ba su gani a kasa ba.

Shugaban dai zai fafata ne da Janar Muhammadu Buhari, dan takara a jam'iyyar adawa ta APC.

Shugaban dai ya ce ya gudanar da ayyuka da dama na ci gaban kasar shi ya sa yake so a sake zabensa.

Sai dai 'yan kasar na ci gaba da sukarsa saboda abin da suka ce gazawarsa wajen magance rashin tsaro da daurewa cin hanci da rashawa gindi.