Cin hanci ya dabaibaye Jonathan - Tambuwal

Hukumar EFCC ta Nijeriya Hakkin mallakar hoto efcc website
Image caption Hukumar EFCC ta Nijeriya

A Najeriya, Majalisar Wakilan kasar ta ce 'yan Najeriyar za su yi mamaki matuka idan aka bayyana musu yadda cin-hanci-da rashawa ya yi katutu a gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan.

Kakakin MajalisarAlhaji Aminu Tambuwal -- wanda ya yi wannan zargi a lokacin da aka kaddamar da yakin neman zaben babbar jam'iyyar adawa ta APC -- ya ce irin cin-hancin da suka gani a cikin shekaru uku da rabi da suka gabata, bai cancanci gwamnatin PDP ta mulki kasar nan ba.

Hon. Jagaba Adams Jagaba, shugaban kwamitin yaki da cin hanci da rashawa na majalisar, ya shaida ma BBC cewar, babu abin da suka iya yi illa bincike da mika wa hukumar zartaswa wadanda suke zargi.

Mr Jagaban ya ce hakkin hukumar zartaswa ne ta gurfanar da su, a hukunta su, amma kuma ya ce ba ta yi hakan ba.

Karin bayani