Batanci: An harbe wani mutum a Pakistan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dokar Pakistna ta amince a kashe duk wanda ya yi batanci

'Yan sanda a kasar Pakistan sun an harbe wani mutum da ake zargi da batanci, kwanaki kadan bayan an sako shi daga gidan kurkuku.

An tsare Abid Mehmood na tsawon shekaru fiye da uku, bayan ya yi ikirarin cewa shi annabi ne.

Kuma an sake shi a 'yan kwanakin nan bayan likitoci sun ba da tabbacin cewa yana da tabin hankali.

Sai dai babu tabbaci game da dalilin da yasa aka kashe shi, ko da yake batanci babban laifi ne a kasar.