Amurka ta gano sabon maganin kwayoyin cuta

Mganin yaki da kwayoyin cuta Hakkin mallakar hoto SPA
Image caption Mganin yaki da kwayoyin cuta

Ga alama wahalar da aka kwashe tsawon shekaru ana yi ta gano maganin yaki da kwayoyin cuta masu bijire ma magunguna ta kawo karshe - bayan da masana kimiyya na Amurka suka cimma nasara ta wannan fuska.

Hanyar da suka bi ta kirkirar wata cuta, ta kai su ga samun nasarar gano wasu magungunan yaki da kwayoyin cuta 25, amma daya daga cikinsu ba bu ko shakka zai yi aiki.

Tun kimanin shekaru talatin da suka wuce ne aka ci nasarar gano wasu sabbin magunguna masu yaki da kwayoyin cuta.

Nazarin wanda aka buga a Mujallar Kimiyya an bayyana shi a matsayin "mai canza salon wasa" kuma kwararru sun yi imanin cewar kadan ta rage kawai a kai ga maganin kwayoyin cuta.

A shekarun 1950 da 1960 aka yi ta kokarin gano magunguna na kwayoyin cuta, to amma babu abinda aka gano har a shekarar 1987 wanda ya hana marar sa lafiya shiga hannun likitoci.

Tun lokacin akwai kwayoyin cututtukan da ba a gani wadanda ske bijire ma magunguna. Cuta kamar ta tarin-fuka tana bijire ma kusan kowanne irin magani.

Masu binciken a Jami'ar Northeastern dake Boston a Massachusetts sun juya ga amfani da kasa wadda kusan daga cikin ta duk wasu kwayoyin cuta ke tasowa.

An yi amfani da naura ta binciken kwayoyin cuta, to amma kashi daya bisa dari kawai za a iya shukawa a dakin bincike.

Tawagar likitocin suka kirkiro wata matattarar kwayoyin cuta. An sanya kwacce irin kwayar cutar a dakuna dabam-dabam, an kuma binne naurar da aka dasa su a ciki.

Ta bayar da damar kasar ta cika dakin da wari na kwayar cutar, tare da bayar da damar nazari a kan ta.

Karin bayani