Amnesty na so a binciki hari kan Baga

Jami'an kungiyar Amnesty a Motar su Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jami'an kungiyar Amnesty a Motar su

Kungiyar Amnesty International ta nemi a binciki kisan gillar da aka yi zargin 'yan Boko Haram sun yi a garin Baga na jihar Bono.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta bayyana damuwa game da rahotannin kisan gillar da ake zargin 'yan kungiyar ta Boko Haram sun yi wa fararen hula masu matukar yawa.

Amnesty International ta yi kira ga gwamnati Najeriya da ta gudanar da bincike kan wannan zargi.

Rahotanni dai na cewa dubban mutane aka kashe a harin nan Baga, wanda aka kai tun daga ranar Asabar ta makon jiya.

Karin bayani