2015: Jonathan da Buhari sun ja zare

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan na PDP

Manyan 'yan takarar shugabancin Nigeria a zaben 2015 sun soma gangamin zawarcin masu kada kuri'a.

A ranar Talata, dan takarar jam'iyyar adawa ta APC, Janar Muhammadu Buhari ya kaddamar da kamfe dinsa a birnin Fatakwal na jihar Ribas.

Shi kuwa shugaban kasar, Goodluck Ebele Jonathan na jam'iyyar PDP sai a ranar Alhamis ya kaddamar da kamfe a birnin Lagos cibiyar kasuwancin Nigeria.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Janar Muhammadu Buhari na APC

Dan takarar jam'iyyar adawa, Janar Buhari ya maida hankali a lokacin gangaminsa ne wajen cewa zai yaki cin hanci da rashawa da kuma tabbatar da tsaron al'umma.

A yayin da Mr Jonathan ke cewa a kara ba shi dama domin ya ci gaba da ayyukan da ya soma domin ciyar da Nigeria gaba.

'Tattalin Arziki da Tsaro'

Batun tattalin arziki da na tsaro su ne abubuwan da za su fi jan hankalin masu kada kuri'a a zaben watan Fabarairun 2015.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Abubakar Shekau na Boko Haram

Faduwar farashin danyen man fetur a kasuwannin duniya ya janyo tsaiko a harkokin tafiyar da ayyukan gwamnati a Nigeria abin da ya kai ga wasu jihohin kasar sun kasa biyan albashin ma'aikata.

Matsalar tsaro musamman a yankin arewa-maso-gabashin kasar na daga cikin kalubalen da kasar ke fuskanta inda 'yan Boko Haram suka kwace wasu 'yankunan kasar.

Rikicin Boko Haram ya raba mutane kusan miliyan daya da muhallansu a jihohin Adamawa da Borno da kuma Yobe.

Tun a shekara ta 2009 da aka soma tashin hankalin, bayanai sun mutane 13,000 ne aka kashe.

Za a iya cewa duk wanda ya lashe zaben 2015 na da kalubale a gabansa domin ganin ya warware wa 'yan kasar matsalolin da ake addabarsu.