Charlie Hebdo: An kashe 'yan binbiga

Hakkin mallakar hoto
Image caption 'Yan sanda sun shafe kwanaki uku suna farautar 'yan bindigar

'Yan sanda a Faransa sun kutsa cikin inda aka yi garkuwa da mutane biyu a Paris da kuma wani birni a arewacin kasar.

An ji karar harbe-harbe da kuma fashewar abubuwa a wani kamfanin dab'i da ke Dammartin-en-Goele, inda ake tunanin wadanda suka aikata kisan Charlie Hebdo suka yi garkuwa da mutum daya.

Kafafen yada labaru a Faransa sun ce an kashe 'yan uwan biyu watau Cherif da Said Kouachi a lamarin.

Jami'an tsaro dai na ta kai-kawo a garin Dammatin-en-Goele, inda aka yi wa Sayyed da Sherif Kuwaci rufin-ganga, a cikin wani gini na wani kamfanin Dab'i.

An kuma ji karar fashewar abubuwa a wani shago da ke gabashin Paris a birnin Porte de Vincennes.

A nan ana zargin wani dan bindiga ya yi garkuwa da mutane.