Faransa: Jami'an tsaro sun yi wa wasu kawanya

Hakkin mallakar hoto
Image caption A ranar Laraba ne wasu 'yan bindiga suka kai hari gidan mujallar Shali Hebdo in da mutane 12 suka rasa rayukansu.

Jami'an tsaron Faransa sun yi wa wasu 'yan uwan juna biyu da ake zargi da kai hari a mujallar Charlie Hebdo a ranar Laraba kawanya.

Ana cigaba da neman 'yan uwan ne a garin Dammartin-en-Goele, in da suke boye cikin wani gini mallakar kamfanin buga takardu.

Rahotanni sun ce 'yan sanda sun yi magana da 'yan uwan da ke yin garkuwa da wani mutum a yanzu haka.

Bayanai na cewa 'yan uwan sun ce a shirye suke su mutu. Kuma hukumomi sun umarci mutanen yankin da su kasance cikin gidajensu tare da kashe fitilu.

Yanayin tsaro dai a garin na Dammartin-en-Goele, ya shafi zirga-zirgar jirage a babban filin jiragen sama na Paris da ke kusa da garin.

'Alaka da Al-Qa'eda'

Jami'an Amurka da na Tarayyar Turai, sun bayyana cewa daya daga mutanen da ake zargi da kai harin ya taba zuwa kasar Yemen a shekarar 2011 domin neman horo a wajen mayakan sa kai na Islama.

Hukumomin Yemen sun ce suna kokarin gano ko Sa'id Koushi na da alaka da 'yan kungiyar Al Qaeda da ke yankin kasashen Larabawa.

Yayin da wasu bayanai ke nuna cewa an taba kulle dan uwansa Sheriff Koushi a gidan yari na tsawon shekaru uku a shekarar 2008 bayan da aka same shi da laifin taimakawa mayaka zuwa Iraqi domin yin fada.