Na'urar magance shanyewar jiki ta yi aiki akan bera

Implant
Image caption Masana kimiyya sun ce wannan babban ci gaba ne a fannin kimiyya

Masana kimiyya sun ce an samu wata na'ura da ta sa wani bera mai shanyayyen jiki ya koma yin tafiya.

Na'urar an dasa ta ne a jikin beran inda daga baya ya fara tafiya bayan da jikinsa ya shanye.

Bincike a fannin na'urar da ake dasawa a kokarin magance matsalar shanyewar jiki, wani fannin ne da ke samun bunkasa.

Sai dai wasu daga cikin na'urorin, sukan zo da matsala inda suke lalata wani bangaren jiki, su kuma daina yin aiki daga baya.

Wata tawagar masana kimiyya daga kwalejin fasaha ta tarayya dake Lausanne (EPEL) ne suka samar da na'urar wacce kan iya yin aikin na wasu watanni.

Kwararru sun bayyana wannan sakamakon bincike a matsayin wata babbar nasara a fannin kimiyya.

A mafi yawan lokuta, raunukan da ake samu a kashin baya ne ke haddasa shanyewar wani bangaren jiki kamar yadda bincike ya nuna.

Hakan kuma na faruwa ne saboda kashin bayan bai aikewa da sako daga kwakwalwa zuwa kafafuwa.