Jonathan ya ce an yi yunkurin kashe shi

Image caption 'Yan kasar na ganin cewa Mista Jonathan ya yi zargin ne saboda ya raba-gari da kungiyar ta MEND

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya yi zargin cewa kungiyar masu fafutika ta yankin Naija Delta, MEND ta yi yunkurin hallaka shi.

Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da yake kaddamar da yakin neman zabensa a jihar Lagos ranar Alhamis.

Mista Jonathan ya ce an yi hayar shugaban kungiyar, Henry Okah, ya kashe shi a ranar daya ga watan Oktoba, 2010 lokacin bikin cikar kasar shekaru 50.

Sai dai a wata sanarwa da kungiyar ta fitar ranar Juma'a, ta ce zargin da shugaba Jonathan ya yi ba gaskiya ba ne, tana mai cewa ya kawo shaidun da za su nuna hakan.

Kungiyar dai ta yi ikirarin cewa ita ce ta kai harin, amma a wancan lokacin shugaba Jonathan ya dage cewa ba ita ce ta kai shi ba.

A wannan makon ne dai kungiyar ta bukaci 'yan kasar su zabi Janar Muhammadu Buhari, tana mai yin suka kan shugaba Jonathan, wanda ta ce yana daurewa masu cin hanci da rashawa gindi.

Masu sharhi dai na ganin cewa shugaban ya yi wannan zargi ne kawai domin sun raba-gari da kungiyar, suna masu cewa idan zargin gaskiya ne mai ya sa sai yanzu yake fada.