Nijar da Chadi zasu gina bututun mai

Hakkin mallakar hoto AFP

Nijar ta cimma yarjejeniya da kasar Chadi don gina bututun mai.

Bututun mai tsawon kilimita dari tara zai tashi daga Nijar ya shiga Chadi kafun ya kai tashar jiragen ruwan Kribi a kasar Kamaru.

A jiya ne ministotcin man kasashen biyu suka cimma yarjejeniyar.

A watan Oktobar shekara ta 2016 ne hukumomin kasar ke sa ran soma fitar da danyen man kasar zuwa kasashen waje.

Ministan man fetur na Nijar Malam Fumakwai Gado ya shaidawa sahen Hausa na BBC cewa "Fatan shugabannin kasashen biyu dai shine yadda za a samu a kammala aikin nan da shekara mai zuwa."