Wata cuta ta fada ma itatuwan Zaitun a Turai

Itatuwan Zaitun

Asalin hoton, bbc

Bayanan hoto,

Itatuwan Zaitun

Ana fargabar mummunan sakamakon da zai iya afka ma itacen zaitun a Turai idan wata cuta ta cigaba da yaduwa ga itatuwan.

Kwararu sun yi kashedin cewa cutar tana tsotse abincin da itacen na zaitun ke samu daga kasa, wannan kuwa babbar barazana ce ga itatuwan.

Mummunan sakamakon da ya hada da samar da karancin 'ya'yan itacen da matakai masu tsada na ciwo kan yaduwar cuta ga itacen sune abubuwan da hakan zai haifar idan cutar ta cigaba da yaduwa ga itacen na zaitun a sassa dabam-dabam na nahiyar Turan masu arzikin man zaitun.

Wannan cuta tana shafar yanki mai dama a kudancin kasar Italy kuma tana da wasu cututtukan mabiya tare da ita, wannan cuta dai ana ganin alamun za ta cigaba da yaduwa.

A wani rahoto ne da hukumar kula da lafiyar abinci ta Turai ta bayar aka yi wannan gargadin.

Hukumar ta lura cewa, annobar kwayoyin cutar dake haddasa mutuwar itacen na zaitun babbar matsala ce ga Trayyar Turai.

Cutar tana iya yaduwa a yankunan da ake hasashen za ta iya afkuwa da za ran, abokan tafiyar ta sun samu yanayin da za su iya cin karensu babu babbaka.

Cutar da ake kira "X fastidiosa" za ta iya shafar tsirrai da dama a Tarayyar Turai kamar su Citrus da grapevine da Stone fruit, kuma za ta iya shafar itatuwa da dama kamar su oak,sycamore da oleander.

Annobar wannan nau'in cutar da ta taba barkewa a arewaci da kudancin Amurka ta nuna irin bannar da za ta iya haddasawa.

Za ta iya yaduwa cikin hanzari a cewar Stephen Parnell wani masanin cututtuka daga Jami'ar Salford da kuma wani mamba dake cikin kwamitin wanda ya bayar da gudunmuwa ga binciken da kwamitin EFSA ya gudanar a kan lafiyar tsirrai.