Bama-bamai sun tashi a Borno da Yobe

Hakkin mallakar hoto AP

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin jahar Borno da ke arewacin Najeriya na cewa, wanni bam ya tashi a babbar kasuwa ta Monday market da ke tsakiyar birnin.

Lamarin ya hallaka mutane, ya jikkata wasu dadama.

Wani jami'in asibiti a birnin ya shaidawa sashen Hausa na BBC cewa: "an kawo musu gawarwaki 15 kuma wasu dadama sun samu raunuka."

Jami'in ya kuma ce suna bukatar taimakon jini, don haka yayi kira ga jama'a da su je su bada gudunmawar jinin.

Ana samun bayanai masu cin karo da juna akan tashin bam din.

Yayinda wasu ke cewa wata yarinya ce ta yi kunar bakin wake, wasu na cewa dasa bam din aka yi.

Ko watan Yulin bara ma wani bam da ya tashi a kasuwar ya kuma hallaka mutane 18 a birnin.

A jihar Yobe ma mai makwabtaka da Borno ma wani bam ya tashi a ofishin 'yan sanda a garin Potiskum.

Rohotanni sun ce a kalla jami'an 'yan sanda biyu sun rasa rayukansu, kuma wasu biyar sun samu raunika.

Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya data dauki alhakin kai harin.