'Yan gudun hijira suna cikin mummunan hali

'Yan gudun hijira na Nijeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan gudun hijira na Nijeriya

A makon da ya gabata ne 'yan kungiyar Boko Haram suka kai munanan hare-hare a jihohin Yobe da Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Daya daga cikin haren-haren dai shine na Baga, inda mayakan kungiyar suka kama garin da sansanin sojin hadin gwiwa na kasashen dake yankin tafkin Chadi.

Harin na Baga ya yi sanadiyyar hallaka mutane da dama da bannata dukiya, ya kuma haifar da kwararar 'yan gudun hijira zuwa sassan yankin da ma kasar Chadi.

Sanata Maina Ma'aji Lawan dake wakiltar yankin da aka kai hare-haren, yana ziyarar sansanonin da 'yan gudun hijrar suke, ya kuma bayyana cewar suna cikin wani mummunan yanayi na fitgita da kuncin rayuwa.

Karin bayani