An sake kai hari garin Potiskum

Wasu majiyyata na karbar magani a asibitin Jihar Yobe Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jihar Yobe ta sha fuskantar hare-haren kungiyar Boko Haram.

Wasu da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne sun sake afkawa garin Potiskum a jihar Yobe.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce bama-bamai biyu ne suka tashi kuma duka mata ne suka kai harin, a kusa da gidan daukar hoto na Photo Place wurin da 'yan siyasa ke yawan zama.

Rahotanni sun bayyana cewar matan sun zo ne a cikin babur din nan mai-taya uku,wato keke-Napep, inda bam na farko ya tashi a cikinsa, ya yin da dayan kuma ya tashi a daidai lokacin da daya 'yar kunar bakin waken ta doshi gidan daukar hoton.

Akalla mutane 4 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu mutane arba'in suka jikkata, suna kuma kwance a babban asibitin jihar.

Ko a ranar Asabar ma 'yan sanda biyu sun rasa rayukansu a jihar ta Yobe, sakamakon binciken wata mota da suke yi inda bam ya tashi da su.