Amurka ta ci Honda tarar dala miliyan 70

Motar Honda Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Motar Honda

Amurka ta ci Kamfanin Honda tarar dala miliyan 70 saboda gazawar sa ta kai rahotannin mace-macen da aka yi sakamakon hadurra

Gazawar Kamfanin Honda na kai rahoto ga hukumomi a Amurka ya sanya an ci tarar kamfanin dala miliyan 70.

A cikin watan Nuwamba, kamfanin Honda ya amsa cewar bai bayar da rahoton hadurra 1,729 ba da suka hada da mace-mace da munanan raunuka a tsakanin watan Yuli na shekara ta 2003 da watan Yuni na shekara ta 2014.

Kamfanin dai ya ce zai canza hanyoyin da yake aikawa da rahotanni na cikin gida.

An ci kamfanin na Honda tara biyu dabam-dabam ta dala miliyan 35 kowacce, daya saboda gazawa ta kai rahotannin mace-mace da raunuka, a yayinda dayar kuma ta gazawa ce wajen amsa neman biyan diyya ta abokan huddar kamfanin.

Dukkan wadannan dai, dokokin Amurka sun amince a ci kamfani tara mai tsaurin gaske.

Sakataren sufuri na Amurka Anthony Foxx ya fada a wata sanarwa da ya tura tare da tarar cewa kamfanin Honda da sauran kamfanonin kera motoci suna da alhakin da ya rataya a wuyan su na daukar nauyin kula da lafiyar jama'a, kuma babu wata hujja ta kuskure yin haka.

Karin bayani