Boko Haram ta kai hari a Kamaru

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyar ta kai harin ne da safiyar Litinin

Kungiyar Boko Haram ta sake kai hari a sansanin dakarun tsaro da ake kira BER, a takaice, a garin Kolofata wanda ke kan iyakar Kamaru da Najeriya.

Kungiyar ta kai harin ne da sanyin safiyar ranar Litinin.

Wasu rahotanni, wadanda ba na Hukuma ba na cewa wani soja guda ya mutu, yayin da bangare guda kuma 'yan boko-haram da dama suka halaka, tare da asarar kayan fadansu.

A wannan gari na Kolofata ne, a bara kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da uwar gidan Mataimakin Firaminista Amadou Ali, da kuma wani basarake.