Faransa ta sa dakaru 15,000 cikin damara

Hakkin mallakar hoto AFP Getty Images
Image caption Za a tsaurara tsaro a wurare masu muhimmanci

Faransa ta ce za ta sanya dakarun kusan 15, 000 a shirin ko-ta-kwana domin su kare ta bayan an kai mata hare-haren ta'addanci a kwanaki uku.

Ministan tsaron kasar, Jean-Yves Le Drian, ya ce za su tsaurara tsaro a yankunan da ya ce "suna da matukar muhimmanci."

Ya ce kara da cewa rabin jami'an tsaron za su kare makarantun Yahudawa guda 700.

Fira Ministan kasar, Manuel Valls, ya ce tabbas Amedy Coulibaly -- dan bindigar da ya kashe mutane hudu a wata kasuwar Yahudawa -- yana da abokan da suke taimaka masa.