Boko Haram: An zargi Turai da kawar da kai

Mayakan kungiyar Boko Haram Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mayakan kungiyar Boko Haram

Wani shugaban cocin Katolika a Nigeria ya zargi kasashen Turai da kawar da kai game da barazanar mayakan kungiyar Boko Haram.

Archibishop na cocin Katolika, Ignatius Kaigama, ya ce tilas kasashen su nuna cewa da gaske suke wajen kawo karshen hare haren da kungiyar ke kai wa a Nigeria.

Ya ce irin wannan damuwa da suka nuna kamata ya yi su rika nunata a duk inda hari ya abku ba wai sai lallai a kasashen Turai ba, idan ya faru a Nigeria da Niger da Kamaru, da kuma sauran kasashe matalauta, ya kamata mu hada karfi wajen tunkarar 'yan ta'adda wadanda ke tayar da hankulan jama'a .

Ya kuma yi kira ga kasashen duniya da su nuna goyon baya da hadin kai don magance wannan matsala kamar yadda suka nuna a hare haren da aka kai a kasar Faransa.