Kungiyar IS ta yi wa Centcom kutse

Image caption Mayakan IS sun gargadi sojojin Amurka cewa sunanan tafe

Wata kungiya dake goyon bayan mayakan IS ta yi kuste a shafin Twitter na rundunar tsaron Amurka Centcom.

Kungiyar ta rubuta sako a shafin Twitan rundunar tsaron cewa "sojojin Amurka, ku sani muna nan tafe, saboda haka ku sa ido".

Sakon yana dauke da sa hannun kungiyar ISIS, sannan kuma wasu bayanan rundunar sun bayyana a shafin Twitan.

Rundunar ta Centcom ta ce tana daukan matakan da suka dace.

Shafin Twitan wanda aka saba bada bayanan hare-haren da sojojin ke kai wa mayakan kungiyar IS ta sama, an rufe shi daga baya.

Kutsen ya auku ne a lokacin da shugaba Barack Obama ya ke gabatar da jawabi a kan matakan yaki da kuste a intanet.

Shugaba Omaba wanda ya yi nuni da kutsen da aka yi wa kamfanin shirya fina finai na Sony, ya ce harin ya tunatar da Amurka irin haduran da take fuskanta da suka shafi tattalin arziki.

Kakakin Obama, Josh Earnest ya ce Amurka tana gudanar da bincike a game da kusten na rundunar Centcom.

Masu kusten sun sanya wasu bayanai a shafin Twitan da nufin bayyana asirin rundunar tsaron, da kuma tsawirori