An yi wa sojojin Amurka kutse ta intanet

Tambarin Kungiyar Hakkin mallakar hoto
Image caption Tambarin Kungiyar

Wata kungiya da ta ce tana aiki a madadin kungiyar kasar musulunci ta yi satar shiga shafin Twitter da na Youtube na cibiyar bada umarni ta rundunar sojin Amurka.

Kungiyar wadda ke kiran kanta Cybercaliphate ta wallafa bayanan tsoffin janar din sojin a shafin na Twitter.

Mai magana da yawun fadar gwamnatin Amurka Josh Earnest ya shaidawa manema labarai cewa lamarin ba wani babba ba ne.

Ya ce zan wannan abu ne da suke gani kullum, kuma abu ne da suka dauka da muhimmanci.

Sai dai akwai bukatar yin taka tsantsan yayin da ake yada labarin.

A karshe ya ce akwai bambanci tsakanin saba ka'idar kundin bayanai, da kuma kutse na wani shafin Twitter saboda haka suna nazarin lamarin domin tantance girman tasirinsa.