2015: Buhari ya yi wa Jonathan raddi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Janar Buhari ya ce Jonathan ba zai iya shugabanci ba

Dan takarar shugabancin Najeriya a karkashin jam'iyyar APC, Muhammadu Buhari, ya ce shugaba Goodluck Jonathan bai san abin da yake yi ba shi ya sa ya ce Buharin bai saya wa soji ko da bindiga ba a lokacin da ya yi shugabancin kasar.

Janar Buhari ya ce, " Wannan [kalami na Jonathan] jahilci ne; wata 20 kawai muka yi [muna mulki], kuma a cikin wata ashirin din nan, ya je ya tambaya jiragen sama nawa muka saya, ba ma bindiga ba. Saboda haka bai san abin da yake yi ba."

Buhari ya nesanta kansa da harin da wasu suka kai wa 'yan hamayya.

Ya ce bai amince da tashin hankali ba, don haka duk wani mai goyon bayansa da ya yi tashin hankali ba da amincewarsa ya yi ba.