Mujallar Charlie tana son tunzura Musulmai

Hakkin mallakar hoto .
Image caption A shekarar 2011, mujallar Charlie ta fara wallafa zanen barkwanci game da Annabi Mohammad (SAW)

Mujallar Charlie Hebdo ta kasar Faransa ta wallafa wani zanen barkwanci da ta nuna fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW) a shafinta na farko.

Mujallar ta buga zanen ne tare da rubutun da ke cewa "an yafe komai", a bugun da za ta fitar ranar Laraba.

Mutumin da mujallar ta yi barkwancinsa ya na rike da wani rubutu, da ke cewa 'ni ne Charlie', kuma a kasan rubutun wani rubutun ne da ke cewa 'an yafe komai'.

Lauyan mujallar Richard Malka ya ce sun yi hakan ne domin su nuna cewa ma'aikatan mujallar Charlie Hebdo ba za su bayar da kai ga masu tsattsaurar akidar musulunci ba.

A ranar Larabar da ta gabata ne wasu 'yan bindiga suka kaddamar da hari a ofishin mujallar, inda suka kashe mutane 12 ciki har da ma'aikatanta 12.

Ana ganin 'yan bindigar sun kai harin ne saboda kasassabar da mujallar ta yi na wallafa wani zanen barkwanci na fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW) a 2011.