Valls: Faransa tana bukatar tsaurara tsaro

Janazar 'yan sanda da aka kashe

Firayim Ministan Faransa, Manuel Valls, ya bayyana cewa akwai bukatar a tsaurara matakan tsaro a kasar, yana jaddada cewa kasar Faransa na fada ne da masu ta-da-kayar-baya, ba da addinin Musulunci ba.

Ya ce ba a canza wa tuwo suna, ya kamata mu bayyana al'amura yadda suke.

A zahiri Faransa na yaki ne da ta'addanci da kuma tsaurin ra'ayi.

Faransa ba ta yaki da addinin Musulunci ko Musulmi.

Tun da farko shugaban kasar, Francois Hollande, ya jagoranci bikin karrama 'yan sanda ukun da aka kashe a hare-haren, ta hanyar ba su lambar girmamawa mafi daukaka a kasar.

Ma'aikatan mujallar barkwancin nan, wato Charlie Hebdo sun bayyana cewa abin da ke kunshe a shafin farko na wallafar da mujallar za ta yi gobe bai saba da al'adar mujallar ta raha ba.