Kotu ta soke hukunci kan Hosni Mubarak

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Juyin juya hali a 2012 ne ya janyo hambarar da Mubarak a kan mulki

Wata kotu a Masar ta soke hukuncin dauri a gidan yari da aka yanke wa tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak.

Kotun ta ce ba a bi ka'idojin doka ba wajen yanke hukuncin kan zargin almubazzaranci da dukiya.

Ta ba da umurnin a sake gudanar da shari'ar Mr Mubarak da 'ya'yansa biyu wadanda ake yanke musu hukunci a tare.

Lauyoyin Mubarak sun ce watakila a sako shi daga inda ake tsare da shi a asibitin soji da ke birnin Alkahira.

A watan Mayun bara ne, aka yanke wa Mr Mubarak hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari bisa zargin barnata dala miliyan tamanin wajen gyara fadar Shugaban kasa.