Za a zauna lafiya da musulmai a Jamus

Hakkin mallakar hoto d
Image caption Shugabannin Jamus sun sha alwashin runguman kowa batare da la'akari da banbance banbance ba

Shugaban kasar Jamus ya yi amfani da gangamin da aka gudanar a Berlin, inda ya sake bai wa musulman kasar miliyan 4 tabbacin zama lafiya da su.

Shugaba Joachim Gauck ya ce musulmai da wadanda ba musulmai ba a kasar, duk 'yan Jamus ne.

Ya ce 'yan bindigar da suka kai hari a ofishin mujallar Charlie Hebdo a Faransa sun yi hakan ne domin su kawo rabuwar kai, amma hakonsu bai cimma ruwa ba.

Shugabannin addinai da na siyasa da suka hada da shugabar gwamnatin Jamus, Angela Markel sun ajiye flawowi a ofishin jakadancin Faransa a kasar domin nuna jimami ga kisan da aka yi Faransar.

Shugaba Angela Markel da ministocinta zasu halarci gangamin nuna hadin kai da kaunar juna da shugabannin addinin musulunci suka shirya.