Zaben 2015: Sojoji zasu kwato garuruwa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Za a gudanar da zabe a wuraren da jami'an tsaro za si iya zuwa

A Najeriya, hukumomi a kasar sun sha alwashin kwato garuruwan dake hannun kungiyar Boko Haram domin ba jama'ar su damar kada kuri'a a zaben dake tafe.

A cikin watan Fabuwairu ne za a gudanar da babban zabe a kasar, amma har yanzu kungiyar Boko Haram ce ke rike da iko da wasu garuruwa a arewa maso gabashin kasar.

Shugaban cibiyar samar da bayanai kan yaki da ta'addanci a kasar, Mista Mike Omeri ya shaidawa BBC cewa sojoji sun kara kaimi wajen kwato garuruwan daga hannun kungiyar Boko Haram.

Ya bukaci mutane su sa ido sosai domin dakile sabuwar hanyar da kungiyar ta bullo da ita, ta yin amfani da yara da 'yan mata a matsayin 'yan kunar bakin wake.

Kungiyar Boko Haram na cigaba da kai hare hare a wasu jihohin arewacin Najeriya, duk da ikirarin hukumomin kasar cewa ana daukan matakan yaki da ita.