Yadda Nigeria ke kallon macin Paris: 'Kar ku yi watsi da mu'

Kwana daya bayan macin hadin gwiwa da aka yi a Paris, wanda ya samu halartar wasu shugabannin duniya wajen yin tur da harin da aka kai kan mujallar barkwanci ta Charlie Hebdo da kuma kasuwar yahudawa, wani fadan cocin Katolika a Najeriya, Ignatius Kaigama ya zargi kasashen duniya da yin watsi da mutanen da rikicin masu ikirarin kishin addini ya shafa a Afrika.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani mutum a gaban ofishin jakadancin Faransa a Abidjan dauke da kwalin da aka rubuta 'Ni ne Charlie ka da a manta da wadanda rikicin Boko Haram ya shafa'

Rahotanni sun nuna cewa kungiyar Boko Haram ta kashe daruruwan fararen hula a cikin garin Baga da kewaye, a wani jerin hare-haren da suka kai tun daga ranar 3 ga watan Janairu.

Wasu rahotanni na cewa mutanen da aka kashe sun kai 2000.

A lokacin da yake tsokaci game da yadda duniya ta maida martani kan abin da ya faru a Paris da kuma Najeriya, Fada Kaigama ya ce ya kamata kasashen duniya su nuna damuwa ga Najeriya kamar yadda suka nuna wa Faransa bayan hare-haren.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Fada Kaigama na Jos da ke tsakiyar Najeriya, birnin da ke da mazauna Musulmi da Kirista, birnin ya kuma fuskanci hare-haren Boko Haram

Kwanaki tara bayan kai hari a Baga, akwai rahotannin da ke nuna cewa gawawwaki suna yashe a cikin dazuzzukan da ke kewayen garin.

Sai dai yankin yana karkashin ikon 'yan Boko Haram don haka babu wata kafa mai zaman kanta da zata iya tabbatar da yawan mutanen da al'amarin ya shafa.

A ranar Lahadi da daddare ne kuma shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, ya fitar da wata sanarwa inda ya ce ya ji takaicin rahotannin da ke nuna cewa an kashe daruruwan fararen hula a Najeriya.

Wasu dai na kallon cewa sanarwar ta makaro.

A shafin sa da zumunta na Twitter, karkashin taken #BlackLivesMaters wato rayuwar baki na da daraja, an yi suka game da abin da wasu ke ganin munafunci ne na kasashen yamma.

Wani tsokaci a shafin ya ce masu ikirarin kishin addini a Najeriya sun kashe mutanen da yawansu ya rubanya wadanda aka kashe a Paris har sau 125, amma kuma shuru kake ji.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Birnin Baga da ke bakin iyaka da Chadi ya fuskanci hare-haren Boko Haram, an dauki wannan hoton ne a watan Aprilun 2013

Malamin cocin, Kaigama ya shaida wa BBC cewa kisan kiyashin da aka yi a Baga da kewayensa ya nuna cewa sojojin Najeriya ba zasu iya kawo karshen Boko Haram ba. Mataimakiyar editan Afrika a BBC, Josephine Hazeley ta ce 'yan Najeriya a yankin arewa-maso-gabashin kasar na ganin gwamnatin kasar da kuma duniya sun juya musu baya.

Ban da batun rashin nuna damuwa daga kasashen duniya, babu wani macin nuna goyon baya ga mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa a kasar.

Bayan sace 'yan matan nan ne 'yan makaranta da masu ikirarin kishin addinin suka yi wata kungiyar masu fafutuka mai suna, Bring Back Our Girls, ta yi ta yin gangami a kasar.

Shugaban sashen Hausa na BBC, Mansur Liman ya ce masu gangamin sun fuskanci matsin lamba daga hukumomi, inda aka takaita musu zirga-zirga saboda dalilai na tsaro.

Sai dai masu fafutuka a Najeriya sun yi amanna cewa makasudin hakan shi ne gwamnati ba ta jin dadin zanga-zangar saboda yana nuna gazawarta wajen yaki da Boko Haram.