Uganda za ta mika Ongwen ga kotun ICC

Image caption Ongwen ya shafe shekaru da dama tare da 'yan tawaye

Sojin Uganda sun bayyana cewa za a mika kwamandan kungiyar 'yan tawayen LRA, wato Dominic Ongwen ga kotun hukunta laifukan yaki- ICC da ke Hague.

A makon jiya ne Dominic Ongwen ya mika wuya a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya, inda mafi yawan 'yan tawayen LRA ke da sansani.

Dominic Ongwen dai ya zama sojan 'yan tawaye ne tun yana yaro karami, inda sannu a hankali har ya zama babban mukarrabin jagoran kungiyar LRA, Joseph Kony.

Ana dai zargin Dominic Ongwen da aikata laifukan yaki da kuma wasu laifuka ta suka shafi tauye hakkin bil'Adama.