An fitar da hotunan harin Boko Haram a Baga

An lalata fiye da gidaje 3100 a garin Doron Baga

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

An lalata fiye da gidaje 3100 a garin Doron Baga

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta fitar da hotunan da aka dauka daga tauraron dan Adam da ke nuna munin hare haren Boko Haram a Baga da Doron Baga na Najeriya.

Hotunan da aka dauka gabanin kai hare haren da kuma bayan hare-haren sun nuna girman ta'adin da 'yan kungiyar suka yi a garuruwan.

Kungiyar ta ce wannan shi ne hari mafi muni, inda aka lalata gidaje da asibitoci da makarantu.

Hotunan sun nuna an lalata gidaje 620 a Baga, sannan aka lalata gidaje 3100 a Doron Baga.

Kungiyar ta ce daruruwan mutane ne aka kashe da suka hada da mata masu juna biyu, da yara da kuma tsofaffi.

Rahoton kungiyar ya ce mutanen da suka mutu sun haura 150 kamar yadda rundunar sojin Najeriya ta sanar.