Soji na gumurzu da 'yan Boko Haram a Biu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mazauna garin sun ce jami'an tsaron na fafata wa da 'yan Boko Haram

Mazauna garin Biu da ke jihar Borno ta Najeriya sun shaida wa BBC cewa jami'an tsaro na can suna fafata wa da 'yan Boko Haram.

Mazauna garin sun ce 'yan Boko Haram din sun yi yunkurin shiga garin ne sai jami'an tsaro suka far musu.

Sun kara da cewa tun da safiyar ranar Laraba ne suka fara jin karar harbe-harben bindigogi da fashewar bama bamai.

Yawancin 'yan gudun hijirar da suka fice daga garuruwansu bayan 'yan Boko Haram sun kwace su dai sun samu mafaka ne a garin na Biu.