An haramta Charlie Hebdo a wasu kasashe

Charlie Hebdo Hakkin mallakar hoto AP

Wata kotu a Turkiya ta bayar da umarnin toshe shafukan intanet d ake dauke da hoton shafin farko na mujallar Charlie Hebdo da aka sake wallafawa bayan harin da aka kai wa ofishin mujallar ta Faransa a makon jiya.

Shafin farko na dauke da zanen Manzon Allah yana alhinin mutane goma sha biyun da aka kashe.

Alkalin kotun ya bayyana zanen da cewa cin mutunci ne, mummunan laifi, kuma sabo.

Mujallar da aka sake wallafawa ta sami kasuwa a wuraren sayar da jaridu a Faransa.

Sai dai kamfanin dillancin labaran Senegal ya ruwaito cewa mujallar ta Charlie Hebdo da aka wallafa ta yau Laraba da kuma jaridar Liberation ta Faransa, wadanda suka sanya zanen Manzon Allah Annabi Muhammad an haramta su a cikin kasar.

An sanya haramcin ne duk da kasancewa shugaban kasar, Macky Sall, yana daga cikin shugabanin da syka halarci macin da aka yi a Paris ta goyon bayan 'yancin fadin albarkacin baki.

Wani wakilin BBC a Dakar ya ce mai yiwuwa an dauki matakin ne saboda sukar da aka rika yi wa Mr Sall na shiga cikin macin.

Hakan nan kuma sake wallafa zanen Manzon Allah da Jaridar ta yi ya kara harzuka jama'a a Senegal.

A jamhuriyar Nijar ma wasu kungiyoyin mata musulmi na kasar sun yi Allah wadai, tare da nuna damuwarsu matuka dangane da muzanta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi wa Sallam, da mujallar ta yi.

Matan Musulmi na kasar ta Nijar na ganin abin da mujalar ta yi ya wuce kima.

Matan sun bayyana wannan matsayin nasu ne dazun nan cikin wata sanarwa da suka fitar a birnin Yamai.