2015: Jonathan, Buhari sun gana kan zabe

Hakkin mallakar hoto State House
Image caption Sun yi kira ga magoya bayansu su kauracewa tayar da zaune tsaye

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da dan takarar shugabancin kasar a jam'iyyar APC Janar Muhammadu Buhari sun gana kan yadda za a kaucewa rikici a zaben 2015.

An yi ganawar ce a karkashin wani shiri mai suna "yadda za a hana aukuwar rikici a zaben 2015", wanda hukumar bunkasa ci gaban kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya ta kira ranar Laraba a Abuja.

A karshen taron 'yan takarar biyu sun sa hannu a kan wata yarjejeniya, wadda ta kunshi wasu matakai na samar da zabe cikin kwanciyar hankali ba tare da wani hargitsi ba.

Tsohon magatakardan Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Annan ne babban bako a taron cimma yarjejeniyar.