2015:An nemi amfani da tsohon katin zabe

Majalisar dokokin Nigeria Hakkin mallakar hoto aliyu
Image caption Majalisar dokokin Nigeria

Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci hukumar zaben kasar wato INEC da ta ba da damar amfani da katin zabe na wucin gadi baya ga na dindindin a ka'idojin ta na gudanar da zaben kasar da ke tafe.

Matakin dai ba ya rasa nasaba da korafe-korafen da ake samu ne a jihohin kasar a aikin da hukumar zaben ke yi na raba katin zaben na dindindin, wanda da shi ne bisa hukumar ta ce za ta yi amfani da shi a zabukan na watan Fabrairu.

Ita dai Hukumar zaben Nigeria INEC ta ce tana ci gaba da aikin rarraba katin zabe na dindindin a dukkanin jihohin kasar.

Batun raba katin zabe na dindindin dai na daga cikin batutuwan da ke kara jan hankulan jama'a yayin da zubukkan kasar ke karatowa.