Samsung ya kaddamar da wayar Z1 a India

Hakkin mallakar hoto Samsung
Image caption Wayar manhajar Tizen tana da karfin batiri fiye da na sauran wayoyi masu farashi daya

Kamfanin wayoyin Samsung ya fara sayar da sabuwar wayar da ya bullo da ita mai amfani da manhajar Tizen.

An fara sayar da wayar Z1 a India a kan kudi dala 92, kuma a cewar kamfanin Samsung, wayar tana saurin wartsakewa idan an kunna ta, sannan batirinta yana dadewa.

A kwanakin baya kamfanin Samsung ya dakatar da shirinsa na fara sayar da wayar a Russia and Japan.

Wani kwararre a fannin fasaha ya ce fara sayar da wayar a India wani mataki ne na fara kaurace wa wayoyin manhajar Android.

Ben Wood na cibiyar tuntuba kan sha'anin fasaha ta CCS Insight ya ce "idan aka kwatanta, wayar Tizen tafi ta Android karfin batiri".

Ya zuwa yanzu, kamfanin Samsung shi ne ke kan gaba a duniya wajen samun cinikin wayoyin Android.

Wayar Tizen tana da na'urar daukan hoto daga baya mai karfin pixel 3.1, sannan daga gaba mai karfin pixel 0.1, sannan kuma tana amfani da layi biyu.

Kamfanin Samsung ya ce wayar Z1 tana bude shafukan intanet da sauri fiye da sauran wayoyi masu farashi iri daya.