Majalisa ta soke tsarin Obama kan baki

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Fadar White House ta yi barazanar nuna karfin ikonta a kan sauye sauyen zaman baki a Amurka

Majalisar wakila a Amurka ta kada kuri'ar soke yunkurin shugaba Obama na yin gyaran fuska ga tsarin shigar baki kasar.

Shugaban Majalisar, John Boehner ya ce yin gaban kansa da shugaba Obama ya yi na aiwatar da sauye-sauyen ba tare da amincewar majalisar ba, wani karan tsaye ne ga dokokin kasar.

Dokar da 'yan majalisar suka kada kuri'a akai, za ta soke umurnin wucin gadi da shugaba Obama ya bayar na jingine batun tasa keyar bakin haure miliyan hudu a kasar zuwa kasashen su.

Fadar White House ta ce abinda 'yan jam'iyyar ta Republican a majalisar suka yi, rashin sanin yakamata ne.

Fadar shugaban kasar ta yi barazanar nuna karfin ikonta wajen cigaba da aiwatar da sauye sayen.