APC ta kwace rinjaye daga PDP a majalisa

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban majalisar wakilai, Aminu Waziri Tambuwal

Jam'iyyar adawa ta APC a Nigeria ta zama mai rinjaye a majalisar wakilan kasar inda ta shiga gaban jam'iyyar PDP mai mulki.

A yanzu APC tana da 'yan majalisar wakilai 179 a yayinda PDP ke da wakilai 162 sai kuma jam'iyyun SDP da APGA da Labour da kuma Accord su ke da wakilai 19 gaba dayansu.

Jam'iyyar APC na kara samun rinjaye ne sakamakon yadda 'yan PDP ke ci gaba da sauya sheka bayan zaben fitar da gwani da aka yi a karshen bara.

A cikin watan Oktobar shekarar da ta wuce ma, shugaban majalisar wakilai, Aminu Waziri Tambuwal ya fice daga PDP ya koma APC.

A cikin watan Fabarairu ne za a gudanar da zabuka a Nigeria kuma tuni 'yan takara suka dage suna zawarcin masu kada kuri'a.