Burtaniya da Amurka za su yaki da ta'addanci

David Cameron da Barack Obama Hakkin mallakar hoto .
Image caption Pry Ministan Burtaniya David Cameron da shugaban Amurka Barack Obama

Burtaniya da Amurka sun sha alwashin hada kai don tunkarar masu tsatsauran kishin Islama bayan harin da aka kai a Faransa inda aka hallaka mutane goma sha bakwai.

A wani sharhi na hadin guiwa da suka buga a jaridar The Times da ke London, Pry Ministan Burtaniya David Cameron da shugaban Amurka Barack Obama, sun ce za su ci gaba da hada kai don yakar duk wasu da ke barazana ga tsarin rayuwar al'ummomin su.

Shugabannin biyu sun kuma jaddada amannar su game da muhimmancin tsaro ga ci gaban tattalin arzikin kasa.

An dai wallafa sharhin ne a jajibirin ziyarar Mr Cameron zuwa birnin Washington.