Faransa za ta kare mabiya duka addinai

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Hollande

Shugaban Faransa Francois Hollande ya ce addinin Islama na tafiya kafada da kafada da dimokradiyya, kuma Faransa za ta kare duka addinai.

A jawabinsa a wata cibiyar kasashen Larabawa a birnin Paris, ya ce kasar ba ruwanta da addini, kuma ta na mutunta dukkan addinai ya kuma lashi takobin daukar tsatsauran matakai kan duk wani wanda ya yi musu barazana.

Mr Hollande ya ce musulmai ne ainihin masu dandana kudar munin tsatstsauran ra'ayi sakamakon rikice-rikice a ko'ina cikin duniya.

Kalaman nasa na zuwa ne bayan kisan mutane 17 da galibi ma'aikatan mujallar nan ma barkawanci Charlie Hebdo ne da wasu masu kaifin kishin Islama suka yi a birnin Paris.