Jonathan ya kai ziyarar ba-zata Maiduguri

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jonathan na son tazarce a karo na biyu

Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan ya kai ziyarar ba-zata zuwa jihar Borno wacce ke fama da rikicin Boko Haram.

Jirgansa ya sauka a birnin Maiduguri, daga nan sai ya wuce barikin Maimalari na runduna ta bakwai inda ya jinjinawa dakarun kasar bisa kokarinsu a yaki da Boko Haram.

Jonathan ya ce "Muna samun nasara wajen samar da kayayyakin aiki tun da aka soma yaki da masu tada kayar baya, kuma za mu ci gaba har sai an samu nasara."

A 'yan makonnin da suka wuce ne 'yan Boko Haram suka yi mummunar barna a Baga inda suka kone gidaje da kuma kashe mutane masu yawa.

Image caption Dubban 'yan gudun hijira na cikin mawuyacin hali

Wannan ne karo na biyu cikin shekaru shida da Mr Jonathan ya ziyarci jihar Borno duk da irin dinbim hasarar rayuka da dukiyoyi da aka yi sakamakon rikicin Boko Haram.

Masu sharhi na ganin ziyarar na da nasaba da siyasa kasancewar Mr Jonathan na kokarin samun mulki a karo na biyu a zaben da za a yi a watan Fabrairu.

Shugaban ya samu rakiyar mai bashi shawara kan harkokin tsaro, Sambo Dasuki da kuma Air Marshal Alex Badeh, babban hafsan dakarun kasar.