Mutane 20 mutu sakamakon kwalara a Rivers

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Hukumomi sun ce mutane 170 suka kamu da cutar

Hukumomi a jihar Rivers da ke kudancin Najeriya sun ce mutane 20 ne suka mutu sanadiyar kamuwa da cutar kwalara.

Kwamishinan lafiya na jihar ya tabbatar wa BBC cewa kimanin mutane 170 ne suka kamu da cutar.

Hukumar lafiya a jihar Rivers ta ce tana kai magunguna da kayan aiki karamar hukumar Andoni, inda lamarin ya faru, domin shawo kan cutar kwalarar da ta barke tsakanin al'umomi kusan goma.

Kusan makonni biyu ke nan da cutar ta bulla a jihar, amma sai yanzu lamarin ya yi kamari.