Boko Haram:Chadi za ta aike da dakaru Kamaru

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojin Kamaru dai sun ce sun kashe 'yan Boko Haram 143 a makon nan

Kasar Chadi ta za aike da dakarunta zuwa Kamaru domin taimaka wa kasar wajen yaki da 'yan Boko Haram.

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya -- wanda ya bayar da wannan sanarwa a ranar Alhamis -- bai bayyana adadin dakarun da Chadi za ta tura kasar ba.

Sanarwar ta ce, "shugaban Chadi Idriss Deby Itno ya amince ya tura dakaru da dama zuwa kasar Kamaru domin hada gwaiwa da dakarunmu wadanda suka dage a yunkurinsu na murkushe 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram".

Sojin Kamaru dai sun ce sun kashe 'yan Boko Haram 143 lokacin da suka kai hari kan sansanin sojin da ke garin Kolofata wanda ke kan iyakar Najeriya da Kamaru.

A ranar Laraba ne dai shugaban na Chadi ya sha alwashin taimaka wa Kamaru da sojin domin su taya ta yakar 'yan Boko Haram .