China na bincike kan cin hanci da rashawa

Shugaba Xi jingping na China Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gwamnatin china na fama da matsalar cin hanci da rashawa a cikin gwamnatin kasar.

Hukumomi a kasar China sun ce ana gudanar da bincike akan, mataimakin ministan tsaron kasar da zargin almundahana.

Shi dai Ma Jian ya shafe kusan shekaru talatin a ma'aikatar tsaron China, ana kuma tuhumarsa da yin amfani da karfin iko ba bisa ka'ada ba.

Wannann dai shi ne bincike mafi girma na baya-bayan nan da za a yiwa Mr Ma, wanda shugaba Xi Jinping ya kaddamar dan yaki da cin hanci da rashawa a kasar.

Haka kuma an tuhumi manyan jami'an gwamnati China da laifuka masu nasaba da irin wanann a kamfe din da Mr Xi yake yi na yakar almundahana da ta maamye gwamnatin kasar China, an kuma garkame wasu daga cikinsu a gidan kaso.

Karin bayani