Boko Haram: ECOWAS za ta kafa runduna

Hakkin mallakar hoto AFP GettyImages
Image caption Makwabtan Najeriya na zaune cikin zullumin hare-hare da Boko Haram

Shugabannin kasashen yammacin Afrika na tunanin kafa wata rundunar hadin gwiwa domin yaki da kungiyar Boko Haram.

Shugaban kungiyar ECOWAS kuma shugaban kasar Ghana, John Dramni Mahama ne ya bayyana haka a ranar Juma'a.

"Ba zai yiwu mu yaki ta'addanci a daidaikunmu ba, dole mu duba hanyar da zamu hada karfi waje guda, mu yi musayar bayanai tare da daidaita dabaru don mu kawar da ta'addanci a baki daya nahiyar Afrika." In ji Mahama.

A mako mai zuwa ne dai ake sa ran kungiyar za ta yi wani taron koli a jamhuriyyar Nijar.