Za a cigaba da noma abinci GM a Turai

Noman abinci GM
Image caption Noman abinci GM

Tarayyar Turai ta baiwa gwamnatocin yankin na Turai karin iko na yanke shawara a kan ko za su noma kayan abinci da aka sauya ma kwayoyin halitta wadanda aka hana nomawa a kasashen Tarayyar Turan.

Majalisar dokoki ta Tarayyar Turan da babban rinjaye ta zartas da wata doka wadda ta baiwa kasashen ta zabin noma irin wadannan nau'oin abincin.

Nau'in Masara MON 810 ita ce kawai nau'in abincin da aka sauya ma kwayoyin halitta da ake nomawa har ma ake fitarwa zuwa kasunnin duniya a Tarayyar Turan.

Kodayake wakilan majalisar dokoki na Tarayyar Turan da Ministoci sun amince da a baiwa kasashe karin 'yanci na zabi, a yanzu saura masana kimiyya su yanke shawara kan wannan batu.

Kayan abincin da aka sauya ma kwayoyin halitta da ake kira GM crops - ana amfani da su kwarai a yankin Amurka da Asia, amma Turawan da dama suna da fargaba kan irin illar da za su iya haifarwa ga lafiyarsu da ta dabbobi.

Wannan shine ke kan gaba cikin manyan batutuwan da aka tattauna kan su a Traon da aka yi tsakanin Tarayyar Turai da Amurka a yarjejeniyar ciniki maras haraji, a yayinda yanayin yadda ake noma wanda ya hada da noman irin wadannan na'uoin abincin a Turai ya bambanta da na Amurka ta Arewa.

Sabuwar dokar dai za ta yi amfani ne kawai a kan nau'oin abinci amma banda nau'oin abincin da ake amfani da su wajen hada abincin dabbobi wanda shi kansa zai iya fadawa cikin jerin na'uouin abinci na bil'adama.

A watan Yulin da ya gabata, sabon Shugaban hukumar Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker ya fada cewar, sauyin ya zamo wajibi saboda a karkashin sabbin dokokin, hukumar tana da hurumi na bayar da ikon shigar da abinci da kuma sarrafa nau'oin abincin da aka sauya ma kwayoyin haliyya ko da kuwa mafi rinjayen mutanen yankin ba su goyon bayan amfani da su.

Kasar Spain ita ce kan gaba a jerin kasashen da ake noma nau'in Masarar nan MON 810 a Tarayyar Turai inda ake noma hecta 338,000 a cewar Tarayyar Turan.

Karin bayani